Isa ga babban shafi
Myanmar

Sojin Myanmar sun gurfanar da Aung San Suu Kyi gaban kotu a karon farko

An gurfanar da hambararriyar shugabar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi gaban kotun kasar ta hoton bidiyo, inda aka fara tuhumarta kan manyan laifuka biyu da ake zarginta da aikatawa, matakin da ke zuwa wata guda bayan juyin mulkin Soji da ya haifar da gagarumar zanga-zangar gama gari.

Wasu mazu zanga-zangar bukatar sakin shugabar gwamnatin Myanmar Aung san Suu Kyi a Myanmar.
Wasu mazu zanga-zangar bukatar sakin shugabar gwamnatin Myanmar Aung san Suu Kyi a Myanmar. AP
Talla

Aung San Suu Kyi wanda aka daina jin duriyar ta ko  ganin ta a bainar jama'a tun bayan da Soji suka kifar da gwamnatin ta a ranar 1 ga watan Fabarairu suka kuma tsare ta, ta bayyana gaban kotun ne ta hoton bidiyo, a daidai lokacin da zanga-zangar neman sakin ta ke ci gaba da mamaye titunan kasar.

Majalisar Dinkin Duniya, wacce tun farko ta yi tir da muzgunawa masu zanga-zangar, ta ce, sojoji sun harbe akalla mutane 18 har lahira a jiya Lahadi.

Suu Kyi, mai shekara 75, Sojin na tuhumarta ne da laifin mallakar na’urar sadarwar tafi da gidanka ta jami’an tsaro ba bisa ka’ida ba, baya ga keta dokokin Coronavirus ta hanyar gudanar da gangamin siysasa,  a lokacin yakin neman zaben bara.

Sai dai Lauyan ta Khin Maung Zaw, ya ce yanzu kuma ta na fuskantar tuhuma kan zargin karya dokokin sadarwa da kuma yunkurin tayar da tarzoma wajen tinzira jama'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.