Isa ga babban shafi
Myanmar-Arangama

Mutane 700 sun mutu a zanga-zangar adawa da sojojin Myanmar

Adadin mutanen da suka mutu a zanga-zangar adawa da sojojin Myanmar ya kai 700, a daidai lokacin da bam ya tashi a Mandalay birni na biyu mafi girma a kasar a karshen mako.

Masu zanga-zanga a Myanmar yayin arrangama da 'yansanda a birnin Mandalay.
Masu zanga-zanga a Myanmar yayin arrangama da 'yansanda a birnin Mandalay. AP - STR
Talla

Myanmar ta tsunduma cikin tashin hankali ne tun bayan da sojojin kasar suka kifar da gwamnatin farar hula ta Aung San Suu Kyi a ranar 1 ga watan Fabairun da ya gabata, yayin da magoya bayanta ke ci gaba da bore, amma sojoji na murkushe su.

Rikicin siyasar kasar na ci gaba da kazancewa duk da kiraye-kirayen da kasashen duniya ke yi na samar da zaman lafiya, inda a ranar Lahadi wani bam da ya tashi a harabar wani banki mallakin sojojin kasar ya raunata jami’in tsaro guda.

Tuni aka baza jami’an tsaro masu yawa a wannan yanki bayan tashin bam din.

Bankin na Myawaddy na daya daga cikin cibiyoyin kasuwancin da sojojin kasar ke tafiyar da alakarsu, amma  fararen hula sun kaurace masa biyo bayan juyin mulkin da suka yi wa Suu Kyi , inda kwastamomi da dama suka ce za su kwashe kudaden ajiyarsu daga bankin.

Wasu masu adawa da mulkin sojojin kasar Myanmar a birnin Yangon.
Wasu masu adawa da mulkin sojojin kasar Myanmar a birnin Yangon. © Reuters

A bangare guda, rahotanni sun ce, ko a ranar Asabar da ta gabata, sai da aka kashe  masu zanga-zanga 82 a  birnin Bago mai tazarar kilomita 40 daga arewa maso gabashin Yangon.

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Myanmar ya ce, yana sanya ido kan abin da ke faruwa a Bago, kuma ya fahimci cewa, an hana bada magani ga wadanda suka jikkata a cewarsa.

Sai dai duk da kisan da ake yi musu, masu zanga-zangar sun ci gaba da fitowa kan tituna don yin tur da sojojin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.