Isa ga babban shafi
Afhanistan-Amurka

Afghanistan na da karfin iya kare kanta daga ta'addanci- Ghani

Shugaban Kasar Afghanistan Ashraf Ghani ya bayyana cewar dakarun tsaron kasar na da cikakkiyar kwarewar da za su iya kare jama’ar kasar daga yan ta’adda bayan ya sanar da tattaunawar da suka yi da shugaban Amurka Joe Biden.

Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani.
Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani. AFP - WAKIL KOHSAR
Talla

Ghani ya ce sun tattauna da Biden kann shirin janye dakarun Amurka daga cikin Afghanistan a farkon watan Satumba, kuma sun mutunta matsayin kasar, yayin da zasu hada kai da kawayen su wajen ganin an janye dakarun cikin kwanciyar hankali.

Shugaban ya ce jami’an tsaron kasar a shirye suke su shawo kan duk wata matsalar tsaron da kan iya tasowa bayan janyewar dakarun na Amurka.

Kusan shekaru 20 kenan Afghanistan ta shafe ta na fuskantar tashe-tashen hankula da hare-haren ta'addanci daga kungiyoyin Taliban, IS da kuma Alqaeda wadanda ke kaddamar da hare-hare kan dakarun Soji da daidaikun fararen hula.

Tun a lokacin Donald Trump, Amurkan ta fara shirin janye dakarun karkashin tattaunawar da ta fara da kungiyar Taliban, sai dai hare-haren da suka faru tare da kisan Sojin Amurkan guda ya ruguza tattaunawar a wancan lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.