Isa ga babban shafi
Syria-Rasha

Dakarun Sojin Rasha sun kashe 'yan tawayen Syria 200 a Palmyra

Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce ta kashe 'yan tawaye akalla 200 a harin saman da ta kai yankin Palmyra da ke kasar Syria inda mayakan ke shirin kai hari a dai dai lokacin da ake shirin gudanar da zaben shugaban kasa.

Wani yanki da ya fuskanci luguden wuta a Syria.
Wani yanki da ya fuskanci luguden wuta a Syria. AP - Hassan Ammar
Talla

Ma’aikatar ta ce bayan samun bayanan asiri daga majiyoyi da dama dangane da wurin da 'yan tawayen su ke, jiragen yakin ta sun kaddamar da hare hare inda suka kashe mutane kimanin 200 da lalata motoci 24 da ke dauke da manyan makamai da kuma kusan kilo 500 na bama bamai.

A ranar 26 ga watan gobe ake shirin gudanar da zaben shugaban kasa wanda shi ne na biyu tun bayan barkewar tashin hankalin da ya biyo bayan zanga zangar juyin juya hali da aka fara a shekarar 2011 wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 388,000, yayinda miliyoyi suka zama ‘yan gudun hijira a kasashen duniya.

Ana saran shugaba Bashar al Assad da ke samun goyan bayan Rasha ya lashe zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.