Isa ga babban shafi
India-Coronavirus

Adadin Indiyawan da suka harbu da Corona ya tasamma miliyan 20

Adadin mutanen da suka kamu da cutar covid-19 a halin yanzu ya tasamma miliyan 20 a kasar India, yayin da kasashen duniya ke ci gaba da taimaka wa kasar da kayayyakin jinya don kula da marasa lafiya.

Sashen kula da masu cutar Corona a jihar Assam.
Sashen kula da masu cutar Corona a jihar Assam. AP - Anupam Nath
Talla

Daga karshen watan maris da ya gabata zuwa jiya litinin kawai, an samu karuwar sama da mutane milyan 8 da suka harbu da wannan cuta a India, matsalar da ta haifar da caccaka ga firaministan kasar wato Nerandra Modi.

Likitoci a jihar Goa da ke yammacin kasar, daya daga cikin yankunan da annobar ta fi tsananta, sun ce yanzu haka asibitoci sun cika makil da marasa lafiya, inda wasu da dama ke kwance a kasa.

Wata babbar matsalar da ake fuskanta ita ce rashin na’uraorin da ke taimaka wa masu dauke da wannan cuta domin yin numfashi, yayin da iskar oxygen ta yi karanci a mafi yawan asibitocin kasar.

A cikin makon da ya gabata ne kasashen duniya da suka hada da Birtaniya, Amurka da kuma Rasha suka fara tura kayayyakin jinya zuwa kasar ta India, yayin da ma’aikatar lafiya ta tabbatar da cewa akalla mutane dubu uku ne ke rasa rayukansu a kowace rana a kasar sakamakon wannan annoba ta Coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.