Isa ga babban shafi
India-Coronavirus

Cutar Korona ta lakume rayukan Indiyawa fiye da dubu 4 cikin kwana 1

Sabbin alkaluman da ma’aikatar lafiyar India ta ta fitar a yau asabar, sun nuna cewar rayukan mutane fiye da dubu 4 annobar Korona ta lakume, yayin da wasuakalla dubu 401 suka kamu da cutar cikin kwana 1 rak a kasar.

Wasu ma'aikatan lafiya a India yayin rarrashin daya daga cikinsu da annobar Korona ta kashe mijinta.
Wasu ma'aikatan lafiya a India yayin rarrashin daya daga cikinsu da annobar Korona ta kashe mijinta. AP - Anupam Nath
Talla

Karin mutanen dubu 4 da 187 da cutar ta kashe, ya sanya jumilar adadin mutanen da suka rasa rayukansu a dalilin annobar kaiwa dubu 238 da 270, yayin da jumilar wadanda suka kamu da ita ya kai kusan miliyan 22.

Karo na farko kenan da adadin ya kai haka tun bayan barkewar annobar a kasar.

Wani mutum dake barci a gefenn hanya sanye da takunkumin rufe baki da hanci a birnin Kolkata na kasar India.
Wani mutum dake barci a gefenn hanya sanye da takunkumin rufe baki da hanci a birnin Kolkata na kasar India. AP - Bikas Das

Sai dai kwarrru sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar adadin mutanen da cutar ta Korona ta kashe da kuma wadanda suka kamu da ita a kasar ta India, ya zarce na alkaluman da ake da su, gami da bayyana fargabar har yanzu annobar da ta sake barkewa karo na biyu ba ta kololuwa ba.

Tuni dai kwararrun Birtaniya suka bayyana damuwa kan sabon nau’in cutar Koronar da ya bulla a India, wanda suka ce yana da hatsari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.