Isa ga babban shafi
India-Guguwa

Mutane 24 sun mutu wasu 100 sun bace a India sakamakon kakkarfar guguwa

Mutane akalla 24 sun rasa rayuaknsu a India, yayin da wasu kusan 100 suka bata a yau Talata, bayan da wata kakkarfar guguwa ta afkawa sassan kasar, a dai dai lokacin da ta ke fama da annobar corona da ke kashe mutane fiye da dubu 4 cikin kowanne sa’o’i 24.

Kakkarfar guguwar kari ne kan annobar covid-19 da ke ci gaba da haddasa asarar dubunnan rayuka a kasar.
Kakkarfar guguwar kari ne kan annobar covid-19 da ke ci gaba da haddasa asarar dubunnan rayuka a kasar. @ompsyram via REUTERS - @ompsyram
Talla

Dubban mutane ne dai suka tagayyara baya ga rasa hasken lantarki, lokacin da guguwar ta afkawa yankunan gabar ruwan jihar Gujarat, inda gwamman mutane suka rasa rayukansu, yayinda wasu da dama suka bace.

Jami’ai sun ce guguwar da aka yiwa lakabi da Tauktae na tsala gudun kilomita 130 a sa’a 1 yayinda ta haddasa murdawar igiyar ruwan da tsawonta ya kai mita 8 a tsaye, wadda ta dulmiyar da wani jirgin ruwan safarar man fetur da masu sikin hakosa a gabar ruwan birnin Mumbai, abinda ya sanya batan mutane 96 daga cikin 273 daga cikin jirgin.

Ma’aikatar tsaron India ta ce zuwa yanzu gidaje fiye da dubu 16 da 500 guguwar ta Tauktae ta rusa, tare da tuge bishiyoyi kimanin dubu 40, sai kuma kauyuka akalla dubu 2 da 400 da suka rasa hasken lantarki.

Kwararru kan binciken lamurran da suka shafi irin wannan masifa, sun ce guguwar ita ce ta baya bayan nan da ta taso daga tekun maliya, wadda ke bayyana yadda matsalar sauyin yanayi ke zafafa ruwan tekun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.