Isa ga babban shafi
Syria

Mutane rabin miliyan sun mutu a Syria

Yakin shekaru 10 a Syria ya lakume rayukan mutane kusan rabin miliyan kamar yadda kungiyar da ke sanya ido a kasar ta bayyana a wannan Talatar, yayin da sabbin alkaluma ke nuna cewa, mutane dubu 100 aka kashe a baya-bayan nan a kasar.

Wani bangare da yaki ya lalata a Syria
Wani bangare da yaki ya lalata a Syria © REUTERS - OMAR SANADIKI
Talla

Kungiyar da ke sanya ido kan hakkin bil’adama a Syria wadda ke da cibiya a Birtaniya ta bayyana cewa, rikicin ya haddasa asarar rayukan mutane dubu 494 da 438 tun bayan barkewarsa a shekarar 2011, yayin da aka yi ta murkushe masu zanga-zangar adawa da gwamnatin kasar.

Alkaluman mamatan da kungiyar ta bayar a cikin watan Maris na bana, sun nuna cewa, sama da mutane dubu 388 aka kashe, amma a yanzu ta tabbatar da samun karin mamata  dubu 105 da 15.

An samu akasarin asarar rayukan ne tsakanin karshen shekarar 2012 zuwa Nuwamban 2015 kamar yadda shugaban kungiyar Rami Abdel Rahman ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.

Sama da fararen hula dubu 42 ne suka mutu daga cikin sabbin alkaluman mamatan da aka tattara , kuma mafi yawansu sun rasa rayukansu ne a sanadiyar azabar da suka sha a hannun sojojin gwamnati a gidajen yari.

Amma a jumulce, fararen hula dubu 159 da 774 aka kashe.

kungiyar ta rawaito cewa, jumullar sojoji da mayakan sa-kai dubu 168 da 326 suka mutu a yakin basasar, yayin da a bangaren mayakan ISIS aka kashe dubu 68 da 393.

Sauran ‘yan tawayen da aka kashe sun kai dubu 79 da 844 a cewar rahoton.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.