Isa ga babban shafi
India-Bollywood

Fitaccen Jarumin India Dilip Kumar ya mutu yana da shekaru 98

Fitaccen Jarumin India Dilip Kumar ya rasu yau Laraba ya na da shekaru 98 a Duniya bayan fama da rashin lafiya, inda tuni fitattun jarumai da ‘yan siyasa suka fara aikewa da sakon ta’aziyya baya ga girmamawa ta musamman ga jarumin da ake kallo a matsayin na musamman.

Fitaccen Jarumin India Dilip Kumar, wanda asalin sunansa shi ne Mohammed Yusuf Khan.
Fitaccen Jarumin India Dilip Kumar, wanda asalin sunansa shi ne Mohammed Yusuf Khan. Roslan RAHMAN AFP/Archivos
Talla

Dilip Kumar wanda asalin sunansa shi ne Mohammed Yusuf Khan an haife shi ranar 11 ga watan Disamban 1922 a Peshawar da ke Pakistan kuma ya fara harkokin fina-finai tun yana da karancin shekaru.

Duk da cewa Kumar bai kasance dan gadon fina-finai ba, amma ya taka rawar gani a sana’ar inda ya yi kaurin suna tsakanin shekarun 1940 zuwa 1960 tare da Dev Anand da kuma Raj Kapoor.

Cikin fiye da shekaru 50 da ya shafe yana fina-finai, Dilip Kumar ya yi fitowa akalla 60 a mabanbantan fina-finan India yayinda ake masa take da na musamman la’akari da kyan sura da kuma fitacciyar muryarshi baya ga salon gashinsa.

Duk da kaurin sunan da ya yi Yusuf Khan ko kuma Dilip Kumar bai samu damar haskawa a matakin Duniya ba, bayan da ya ki amincewa da wani film da aka shirya mai suna Lawrence of Arabia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.