Isa ga babban shafi
Afghanistan - Taliban

Afghanistan ta roki Turai kada ta kori 'yan kasar ta saboda Taliban

Afghanistan ta bukaci kasashen Turai da su dakatar da tilasta maido da ‘yan kasarta dake cin rani a nahiyar ta Turai har tsawon watanni uku masu zuwa, sakamakon zazzafar fafatawa da jami’an tsaron kasar ke yi da mayakan Taliban da yanzu haka suka yi shelar mamaye sama da kashi 85 na kasar.

Sojojin Afganistan tare da motocin yaki a yankin Badghis, ranar 7 ga watan Yuli 2021.
Sojojin Afganistan tare da motocin yaki a yankin Badghis, ranar 7 ga watan Yuli 2021. AP - Mirwis Omari
Talla

Sabon rikici da kasar ke fuskanta ya kara raba dubbun mutane da gidajensu adaidai lokacin da kasar ke fama da sake barkewar annobar korona.

Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya na nuna akwai kusan ‘yan gudun hijirar Afghanistan miliyan biyu da rabi daga shekarar 2018 – amatsayin kasa ta biyu mafi yawan‘ yan gudun hijira a duniya, Mafi yawansu na cikin makwabta Pakistan, sai Iran, da kuma Turai.

Yayinda sama da ‘yan gudun hijirar Afghanistan 570 suka dawo kasar don radin kansu tsakanin watan Janairu zuwa Maris na wannan shekara, wanda Majalisar Dinkin Duniya ta taimaka, shida ne kawai suka zo daga wajen Pakistan da Iran, a cewar bayanai daga hukumar kula da‘ yan gudun hijirar ta Majalisar Dinkin Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.