Isa ga babban shafi
Afghanistan

An yi wa filin jiragen saman Kabul luguden wuta

A yau Litinin aka harba rokoki a filin jirgin saman Kabul, inda dakarun Amurka ke hanzarin kammala janyewa daga Afghanistan tare da kwashe abokansu da ke fuskantar barazanar hare-hare daga kungiyar IS.

Wani mayakin Taliban a harabar filin jiragen saman birnin Kabul
Wani mayakin Taliban a harabar filin jiragen saman birnin Kabul WAKIL KOHSAR AFP
Talla

A ranar Talata, 31 ga watan Agusta ne wa’adin da shugaba Joe Biden ya diba cewa dakarun Amurka za su kammala janyewa daga Afgahnistan ya cika,  abin da ke kawo karshen yakin da suka fi kwashe tsawon lokaci suna yi a tarihi, wanda aka fara shi a matsayin martani ga hare-haren 11 ga watan Satumba ta shekarar 2001.

Dawowar kungiyar Taliban mai tsatsauran ra’ayi kan karagar mulki makonni 2 da suka wuce, bayan da aka hambarar da ita a shekarar 2001, ya sanya dimbim mutanen da suka tsorata suka fara ficewa daga Afghanistan, ta wajen shirin kwashe jama’a da Afghanistan ke jagoranta.

Yanzu dai, dakarun Amurka sun mayar da hankali ne ga karashe barin kasar ta Afghanistan tare da jami’an diflomasiyyarsu.

Kungiyar IS, wadda abokiyar hamayyar Taliban ce, ta kasance babbar barazana ga aikin janyewar, bayan da ta kai hare-hare a wajen filin jirgin saman Kabul  da ya lakume rayuka sama da 100, ciki har da dakarun Amurka 13.

Biden ya yi kashedin cewa, karin hare-hare na nan tafe, bayan da ya ce, kasarsa ta kai hari ta sama a kan wata mota da kungiyar IS ta makare da bam, bayan haka ne a safiyar Litinin aka harba rokoki a filin jirgin saman Kabul.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.