Isa ga babban shafi
India-Nepal

Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 200 a India da Nepal

Alkaluma sun nuna yadda ambaliyar ruwa ta hallaka mutane kusan 200 a India da Nepal dai dai lokacin da masana ke hasashen yiwuwar sake fuskantar mamakon ruwa a nan gaba.

Yadda ambaliyar ruwa ke barna a Nepal.
Yadda ambaliyar ruwa ke barna a Nepal. - AFP
Talla

Ambaliyar ruwan wadda ke samo asali daga mamakon ruwan da aka rika fuskanta cikin ‘yan kwanakin nan a kasashen biyu bayanai sun nuna yadda laka ta zurma da tarin gidaje yayinda ruwa yayin awon gaba da wasu yara mata biyu.

A Nepal kadai bayanai sun nuna yadda mutum 88 suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ciki har wasu mutum 6 iyalan gida guda da ruwan yayi awon gaba da su.

Masana sun alakanta karuwar ambaliyar ruwan a kudancin Asiya cikin ‘yan shekarun nan da sauyin yanayi baya ga matakan da mutane ke dauka na sare bishiyu.

A yankin Himalayan na arewacin India hukumomi sun tabbatar da mutuwar mutum 55 sanadiyar ambaliyar a Uttarakhand yayinda gidaje da dama suka rushe baya ga katsewar lantarki.

Bayanai sun nuna cewa ambaliyar ta lalata manyan tituna a kasashen biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.