Isa ga babban shafi
India

India ta sake bude kofa ga masu yawon bude ido

India ta bai wa masu yawon bude ido na kasashen waje damar kai ziayara, bayan da aka dauki tsawon watanni 20 da rufe wuraren shakatawa saboda barkewar cutar ta Covid-19.

Taj Mahal na daya daga cikin manyan wuraren tarihi da masu yawo bude ido ke ziyarta a India.
Taj Mahal na daya daga cikin manyan wuraren tarihi da masu yawo bude ido ke ziyarta a India. AFP
Talla

Masu gudanar da yawon bude ido sun ce, duk da haka, wannan dama ba ta yi musu yadda suke so ba, saboda tsadar tikiti, sai kuma dokokin da suka hana matafiya daga Biritaniya da China da sauran wurare shiga kasar.

Kasar da ta shahara da wuraren bude ido irin su Taj Mahal, manyan wuraren shakatawa, wuraren ajiyar dabbobin jinsin damisa, a watan Maris din shekarar 2020, gwamnatin kasar ta haramta wa baki daga kasashen waje kai ziyara, bayan da annobar Korona ta kara tsananta a wancan lokacin.

Amma bayan wani mummunan tashin hankali da aka shiga, saboda samun yawaitar masu kamuwa da cutar a farkon wannan shekara, aka fara samun sassaucin, yayin da gwamnatin kasar ta fuskanci kalubale daga masana’antun da ke taka rawa ga tattalin arzikin kasar.

An bada biza na yawon buɗe ido ga baki masu cikakkiyar allurar rigakafi daga kasashen da ke ban gishiri in baka manda da Indiyar damar shiga tun ranar 15 ga watan Oktoba, amma ga wadanda ke daukar shatar jirgi, inda aka fadada wannan damar a yau Litinin.

Wadanda suka fito daga kasashen Biritaniya da wasu kasashen Turai da China da Brazil da Afirka ta Kudu da sauran wurare suna karkashin karin matakan da suka ce, sai an yi gwajin cutar kafin su shiga kasar.

Goa, wanda ya kasance sanannen wurin yawon bude ido a kudancin India, jirgin farko na masu yawaon bude ido da suka fito daga Biritaniya  zai isa yankin a ranar 13 ga Disamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.