Isa ga babban shafi
Korea ta Arewa

Kim Jong Un ya bunkasa sashen nukiliyar Korea ta Arewa cikin shekaru 10

Shekaru 10 bayan karbar ragamar mulkin Korea ta Arewa shugaba Kim Jong Un ya zama babbar barazana ga kasashen yammacin duniya, bayan kalubantarsu ta fuskar gwaje-gwajen makamai masu linzami ba kakkautawa ciki har da gwajin makamin kare dangi guda.

Wani makami da Korea ta Arewa ta yi gwajinsa
Wani makami da Korea ta Arewa ta yi gwajinsa AP
Talla

Kim Jong Un wanda ya karbi ragamar Korea ta Arewa tun yana da shekaru 27 a Duniya yanzu haka ya shiga sahun shugabanni mafiya gogewa ba tare da wata fargabar yiwuwar sauke shi daga mulkin nan da gomman shekaru ba matukar ya na da kosasshiyar lafiyar tafiyar da kasar.

A tsawon shekaru 10 da ya shafe yana mulkin Korea ta Arewa, Kim Jong Un ya mayar da hankali kacokan wajen mallakar muggan makamai duk da takunkuman da ke kan kasar da kuma matsin lambar ganin Korean ba ta fadada makaman da ta ke da su ba.

Tun bayan gadar mulkin kasar daga mahaifinsa Kim Jong na 11 da ya mutu a ranar 17 ga watan Disamban 2011,  Kim Jong Un ya shafe shekaru 6 ba tare da ya taka kafa wajen kasar ba, inya ya kashe kawunsa kan laifin cin amanar kasa bayan auren Jang Song Thaek haka zalika ya kashe yayansa Kim Jong Nam a filin jirgin saman Kuala Lumpur ta hanyar amfani da guba saboda yadda ya ke bashi matsala wajen tafiyar da mulkin kasar.

Cikin sauri sashen muggan makaman Nukiliya ya matukar habaka karkashin mulkin Kim wanda ya yi gwaje-gwajen makamin kare dangi har sau 4 cikin gwaje-gwaje 6 da kasar ta taba yi a tarihi cikin shekarun 2006 da 2009 da 2013 da 2016 sau biyu da kuma 2017 ciki har mafi muni na makamin kare dangi da ya fi tayar da hanklain Duniya.

A 2006 ne Kim Jong Un ya yi wani mummunan gwajin makamin kare dangi da ya seta Amurka gabanin shiga tsakanin Korea ta kudu inda kasar ta fara tattaunawa da shugaban Amurka na wancan lokaci Donald Trump tare da alkawarta kwance wasu makamanta na nukiliya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.