Isa ga babban shafi
India

'Yan sandan India na bincike kan shirin kashe Musulmai

Rundunar ‘yan sandan India ta sanar da fara bincike kan wani taron mabiya addinin Hindu a birnin Haridwar wanda ya tattauna kan yadda za a yi wa Musulmi kisan kiyashi, taron da bayanai ke cewa ya samu halartar wakilcin mamba daga jam’iyyar Firaminista Nrendra Modi.

Wasu jami'an 'yan sandan kasar India
Wasu jami'an 'yan sandan kasar India AP
Talla

Rundunar ‘yan sandan ta India wadda ta samu faifan bidiyon taron na farkon watannan nan a birnin Haridwar mai muhimmanci ga mabiya addinin na Hindu ta ce, tuni sashenta na bincike ya fara bin diddigi don tabbatar da sahihancinsa tare da tunkarar matsalar.

Faifan bidiyon taron na Hindu ya nuno yadda wani jagora ke bayanin cewa kada mabiyansu su ji tsoron zuwa yari don kawai sun kashe Musulmi, yana mai cewa ba zai zame musu asara ba idan suka sadaukar da mabiyan Hindu 100 don zama sojoji tare da taimaka wa wajen kisan Musulmi miliyan 2 don baiwa wurin bauta na Sanatana Dharma kariya.

Bayanai sun ce, taron wanda ya gudana a tsarkakken birnin Haridwar ya samu halartar guda cikin mambobin jam’iyyar Firaminista Narendra Modi ta BJP wadda ta yi kaurin suna wajen kiyayya ga mabiya addinin Islama.

Sai dai tuni jam’iyyar ta BJP ta musanta batun halartar mambanta ga taron. Kodayake ta tabbatar da sahihancin bidiyon tare da goyon bayan gudanar da bincike a kansa.

Wani fitaccen dan Majalisa kasar Asaduddin Owaisi ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa kalaman da ke dauke cikin faifan bidiyon ba komi yak e umarta ba face kisan kare dangi ga mabiya addinin Islama.

Har zuwa yanzu dai gwamnati Modi ba ta yi tsokaci game da taron da kuma fitar faifan bidiyon ba, wanda a cikinsa wata mata ta bukaci mabiyan na Hindu su yi addu’a ga Nathuram Godse wanda ya aikata kisan gilla ga Mahatma Gandhi a shekarar 1948.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.