Isa ga babban shafi
Malaysia

Ambaliyar ruwa ta kori dubban mutane a Malaysia

Dubban mutane ne suka tsere daga gidajensu, yayin da ruwan sama kamar da bakin kwarya ya ta'azzara ambaliya a wasu jihohi bakwai na Malaysia, kamar yadda hukumomin kasar suka tabbatar, al’amarin da ya yi sanadiyyar rayukan mutune 50 ya zuwa yanzu.

Yadda jama'a ke ficewa daga gidajensu saboda ambaliyar ruwa a Malaysia
Yadda jama'a ke ficewa daga gidajensu saboda ambaliyar ruwa a Malaysia AP - Vincent Thian
Talla

Hukumomin kasar dai sun ce,  wannan ambaliyar ruwa ta tilasta kwashe sama da mutane 125,000 daga tsakiyar watan Disamba zuwa yanzu.

Hukumar Kula da Bala’o’i ta kasar ta ce, ana sa ran za a ci gaba da fuskantar munanan bala’o’i saboda matsalar yanayi ta tsawon makonni.

Kasar da ke kudu maso gabashin Asiya ta fuskanci yanayi mai zafi a karshen shekarar da ta wuce, tare da ambaliya da ta tilastawa jama’a yin kaura.

Sai dai hukumomi sun yi mamakin kwanakin da aka dauka ana tafka ruwan sama, wanda ya fara sauka daga ranar 17 ga watan Disamban da ya wuce, lamarin da ya sanya koguna suka tumbatsa tare da haifar da ambaliya a birane.

Jihar Selangor mafi arziki a Malaysia  wadda kuma ta kasance cibiyar kasuwancin kasar na daga cikin wadanda ambaliyar ta fi kamari.

Kimanin mutane 117,700 daga cikin wadanda aka kwashe tun tsakiyar watan Disamba suka koma gidajensu, ko da yake kusan mutane 10,000 a jihohi biyar na kasar da kuma jihar Sabah da ke tsibirin Borneo sun nemi mafaka a cibiyoyin bayar agaji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.