Isa ga babban shafi
Korea ta Arewa - Nukiliya

Korea ta Arewa ta sake harba makami mai linzami daga jirgin kasa

Kasashen Korea ta Kudu da Japan, sun ce Korea ta Arewa ta sake harba wani shu’umin makami mai linzami daga jirgin kasa a ranar Juma’a.

Makami mai linzamin da Korea ta Arewa ta harba daga jirgin kasa.
Makami mai linzamin da Korea ta Arewa ta harba daga jirgin kasa. STR KCNA VIA KNS/AFP
Talla

Gwajin harba makamin mai linzami dai shi ne karo na uku da kasar ke yi a makon da ya kare, bayan gwaje gwajen da ta yi a ranakun 5 da kuma 11 ga watan Janairun da muke, duk da takunkumin da ke kanta.

A cikin watan Satumban shekarar 2021 Korea ta Arewa ta soma gwajin harba makami mai linzami.

Cikin makon da ya kare Amurka ta laftawa Korea ta Arewa karin takunkumai karya tattalin arziki, bayan da ta zargi Korean da tsokanar fada da gangan.

Wannan dai na zuwa ne bayan da Korea ta kudu ta gargadi makwafciyar ta ta, kan yadda ta take  takunkuman da aka lafta mata, tare da yin gwaje-gwajen shu’uman makaman.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.