Isa ga babban shafi
Yemen-Huthi

Harin mayakan hadakar kasashen larabawa ya kashe mutane 11 a Yemen

Akalla mutane 11 suka mutu a wani harin dakarun hadakar kasashen larabawa yau talata a Yemen farmakin da ke matsayin ramuwa ga harin ‘yan tawayen Huthi da ya hallaka mutane 3 a hadaddiyar daular larabawa.

Yankin da dakarun hadakar kasashen larabawa suka farmaka a birnin Sanaa na Yemen.
Yankin da dakarun hadakar kasashen larabawa suka farmaka a birnin Sanaa na Yemen. MOHAMMED HUWAIS AFP
Talla

Wasu ganau da kuma majiyar bangaren lafiya sun tabbatar da farmakin na birnin Sanaa a Yemen harin da aka kaddamar da safiyar yau talata sa’o’I kalilan bayan harin makami mai linzami da kuma jirgi marar matuki da ‘yan tawayen Huthi suka kai birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa tare da hallaka mutane 3.

Wasu hotunan bidiyo bayan farmakin na Yemen sun nuno yadda al’ummar yankin da harin ya faru ke aikin kwashe baraguzan gine-gine don laluben wadanda suka makale a ciki bayan luguden wutar ta sama da sojin na hadakar kasashen larabawa karkashin jagorancin Saudiya suka kaddamar.

Guda cikin ‘yan uwan wadanda harin ya rutsa da su a Sanaa Akram al-Ahdal da ke cikin masu aikin kwashe baraguzan gine-ginen ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa akwai tarin mutanen da suka makale, cike da fargabar yiwuwar su rasa ransu.

Dama Hadaddiyar Daular Larabawa da ke cikin hadakar Sojin Kasashen larabawa bisa jagorancin Saudiya mai yakar ‘yan tawayen na Huthi masu samun goyon bayan Iran ta sha alwashin mayar da marani kan harin na jiya litinin da ke matsayin irinsa na farko da ‘yan tawayen suka kai mata cikin shekaru 7 da aka shafe ana yaki tsakanin bangarorin biyu a Yemen.

Harin na Huthi kan babban birnin kasar ta hadaddiyar Daular laraba ya tayar da hankalin kasashen yankin Gulf dai dai lokacin da yakin bangarorin biyu ke ci gaba da daukar sabon salo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.