Isa ga babban shafi
India

An gano jirgin yakin da ya yi hatsari a India bayan shekaru 77 da bacewarsa

An gano wani jirgin yakin duniya na biyu da ya bace a yankin Himalayas mai nisa na kasar India kusan shekaru 80, bayan da jirgin ya yi hatsari ba tare da an samu wadanda suka tsira ba.

An gano wani jirgin yakin duniya na biyu da ya bace a yankin Himalayas na kasar Indiya kusan shekaru 80 bayan da ya yi hatsari ba tare da fasinjojin da ke cikinsa sun tsira ba.
An gano wani jirgin yakin duniya na biyu da ya bace a yankin Himalayas na kasar Indiya kusan shekaru 80 bayan da ya yi hatsari ba tare da fasinjojin da ke cikinsa sun tsira ba. © MIA Recoveries/AFP
Talla

Bayanai sun ce aikin laluben dadadden jirgin yakin da aka shafe shekaru ana yi, sai da yayi sanadin mutuwar mutane 3 da ke cikin tawagar jami’an da ke neman gano jirgin yakin da ya shefe shekaru 80 da bacewa.

Jirgin kirar C-46 na dauke da mutane 13 ne daga birnin Kunming da ke kudancin kasar Sin a lokacin da ya bace sakamakon rashin kyawun yanayi a tsakanin tsaunukan jihar Arunachal Pradesh a makon farko na shekarar 1945.

Clayton Kuhles, wani dan kasar Amurka da ya jagoranci aikin laluben jirgin yakin da ya bace, ya ce sun fara gudanar da binciken ne, bayan da dan daya daga cikin fasinjojin jiragin yakin da suka mutu ya nemi da su gano inda mahaifinsa ya rasa ransa a lokacin yakin duniyar na 2.

Tawagar masu binciken ta gano jirgin yakin ne a saman wani dutse mai dusar kankara a watan Disambar da ya gabata, inda suka iya tantance tarkacen jirgin ta hanyar gano lambarsa daga bangaren wutsiya.

Sai dai babu ragowar gawar ko da mutum guda a cikin abin da ya rage na baraguzan jirgin yakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.