Isa ga babban shafi
Myanmar

Yau shekara daya bayan juyin mulkin Myanmar

Yau aka cika shekara guda da juyin mulkin da ya kawo karshen dimokiradiya a kasar Myanmar, lokacin da sojoji suka kifar da gwamnatin Aung San Suu Kyi.

Jagorar Myanmar Aung San Suu Kyi da aka hambarar shekara daya da ta wuce.
Jagorar Myanmar Aung San Suu Kyi da aka hambarar shekara daya da ta wuce. STR AFP/File
Talla

Juyin mulkin ya haifar da zanga zangar da ta sanya hallaka mutane sama da 1,500 wadanda suka bijirewa sojojin, suka kuma bukaci mayar da mulki ga fararen hula.

A jawabin shugaban sojin Min Aung Hlaing da aka wallafa yau yace tilasta musu akayi suka karbi iko sakamakon magudin zaben da aka tafka wanda ya bai wa jam’iyyar Suu Kyi nasara.

Shugaban ya yi alkawarin gudanar da karbabben zabe a watan Agustan shekara mai zuwa muddin aka samu zaman lafiya a kasar.

Tuni aka yanke wa Suu Kyi hukuncin daurin shekaru 6 a gidan yari saboda samun ta da laifin shigar da na’urar magana ta barauniyar hanya da tinzira jama’a yi wa sojojin bore da kuma karya dokokin yaki da annobar korona.

An sa ran Suu Kyi ta sake fuskantar shari’a a kan zargin shirya magudin zabe lokacin da jam’iyyar ta samu gagarumar nasara a zaben shekarar 2020.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.