Isa ga babban shafi
China

China ta kulle birni mai yawan mutane fiye da miliyan 3

Dokar kullen hana shiga da fita ta fara aiki kan wani birnin kasar China da ke kusa da iyakar Vietnam mai kunshe da mutane akalla miliyan 3 da rabi,  bayan da aka gano mutane fiye da 70 da suka kamu da cutar Korona, cikin kwanaki ukun da suka gabata.

Wasu jami'an lafiya a kasar China.
Wasu jami'an lafiya a kasar China. © cnsphoto via REUTERS
Talla

Tun bayan samun nasarar dakile yaduwar annobar Korona da ta fara a bulla a cikinta a watan Disambar 2019, kasar China ke cikin shirin ko-ta-kwana don tabbatar da nasarar hana sake bazuwar cutar a yayin da take karbar bakuncin wasannin Olympics na lokacin sanyi a birnin Beijing.

A ranar Lahadin da ta gabata mahukuntan birnin Baise da ke kudancin lardin Guangxi suka sanar da haramta shiga da kuma fita daga cikin birnin, yayin da kuma za a killace mazauna wasu gundumomin da ke karkashin yankin a gidajensu, kamar yadda mataimakin magajin gari Gu Junyan ya shaida wa wani taron manema labarai.

Tun a ranar Juma’ar da ta gabata, mai’aikatan lafiya suka gano wani matafiyi da ya koma gida hutu a matsayin mutum na farko da ya kamu da cutar Korona a birnin Baise, mai tazarar kilomita 100 daga kan iyakar Vietnam.

Tun bayan barkewar annobar a shekarar 2019, China ta gina shingen waya mai karfi a kan iyakarta ta daga bangaren kudanci don hana bakin haure tsallakawa cikinta daga Vietnam da kuma Myanmar domin dakile yaduwar cutar ta Korona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.