Isa ga babban shafi
Iran - Isra'ila-nukiliya

Isra'ila ta ce ba za a samu abin da ake so ba a yarjejeniyar nukiliyar Iran

Firayim Ministan Isra'ila Naftali Bennett ya ce Iran na iya amincewa da sabuwar yarjejeniyar nukiliya da manyan kasashen duniya amma ya yi gargadin cewa da wuya a samun abin da ake fata na fiye da yarjejeniyar da aka kulla a shekarar 2015.

El primer ministro Naftali Bennett preside la reunión semanal del gobierno israelí, el 20 de febrero de 2022 en Jerusalén
El primer ministro Naftali Bennett preside la reunión semanal del gobierno israelí, el 20 de febrero de 2022 en Jerusalén Tsafrir Abayov Pool/AFP
Talla

Shugaban ya yi jawabi ne kan shirin nukiliyar Iran a taron majalisar ministocinsa da kuma wani taron kungiyoyin Yahudawa na Amurka, bayan alamu da ke nuna cewa yarjejeniyar ta fara aiki a tattaunawar da ake yi a Vienna.

Yarjejeniyar Iran ta 2015 ta yi tayin sassaucin takunkumin da aka kakaba mata domin dakile shirinta na nukiliya.

Ko da yake Amurka ta fice daga yarjejeniyar a shekarar 2018 karkashin Shugaba Donald Trump tare da sake sanya mata takunkumin tattalin arziki.

Tattaunawa kan farfado da yarjejeniyar ta sake komawa kan teburi, bayan tazarar watanni da dama a babban birnin kasar Austriya a karshen watan Nuwamba, wanda ka tsaye ya shafi kasashen Birtaniya, China, Faransa, Jamus da Rashada kuma Amurka a fakaice.

Isra'ila ta kasance mai adawa da shirin kuma ta sha gargadin duk wani kudaden shiga da Iran za ta samu sakamakon sabon takunkumin da aka kakaba mata, wanda take ganin za a yi amfani da su wajen siyan makaman da ka iya cutar da Isra'ilawa.

Firaministan Isra'ila, a jawabin da ya yi a taron yahudawa, ya bayyana abubuwan a matsayin damuwa da dama a cikin yarjejeniyar da aka kulla, ba tare da bayyana majiyarsa ba kan abin da tattaunawar ta kunsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.