Isa ga babban shafi
Pakistan

Dan kunar bakin wake a Pakistan ya kashe mutane 56 a masallacin 'yan shi'a

Wani mummunan hari wanda shine irin sa na farko tun shekarar 2018, da aka kai birin Peshawar a yankin arewa maso yammacin Pakistan, a wani masallacin mabiya akidar Shi’a, ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 56 sannan wasu 194 suka jikkata.

Masallacin 'yan Shi'a na garin Pashewar a Pakistan da akak kai harin kunar bakin wake.
Masallacin 'yan Shi'a na garin Pashewar a Pakistan da akak kai harin kunar bakin wake. REUTERS - FAYAZ AZIZ
Talla

Harin wanda aka kai a gabanin sallar Juma’a, ya bar baraguzan gilasai a kan hanyoyin birnin.

Wannan dai na zuwa ne a ranar farko da aka fara gwajin wasan cricket a Pawalpindi, tsakanin Pakistan da Australia wacce ta kwashe shekaru da dama ba tare da ta ziyarci kasar sabida matsalar tsaro.

Mai magana da yawun gwamnatin lardin Khyber Pakhtunkhwa ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa harin na kunar bakin wake ne.

Wani wanda ya shaida harin, Ali Asghar ya ce yaga shigar wani mutum cikin masallacin gabanin sallar Juma’a inda ya ciro karamar bindiga ya fara harbin mutane daya bayan daya.

Babban jami’in ‘yan sandan yankin Muhammad Ijaz Khan, ya shaidawa kamfanin AFP cewa, mutane biyu suka kai harin, kuma ya rutsa da jami’an ‘yan sanda biyu a lokacin shiga masallacin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.