Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falasdinawa

'Yan sandan Isra'ila sun harbe wani Bafalasdine da ya kai musu hari

Rundunar ‘yan sanda Isra’ila ta ce jami’anta  sun kashe wani Bafalasdine bayan da ya daba wa wani jami’i wuka a yau Lahadi.

Wani dan sandan Isra'ila yana gadin inda wanin matashi Bafalasdine ya daba wa jami'ansu 2 wuka a Birnin Kudus.
Wani dan sandan Isra'ila yana gadin inda wanin matashi Bafalasdine ya daba wa jami'ansu 2 wuka a Birnin Kudus. REUTERS/Ammar Awad
Talla

Mutumin ya tinkari jami’an ‘yan sandan da ke gadi a kofar  Bab Huta a Birnin Kudus, inda ya zaro wuka ya daba wa daya daga cikinsu, a cewar sanarwar da rundunar ta fitar, tana mai cewa an harbe maharin mai shekaru 19 har lahira.

Sanarwar maharin ya ji wani dan sanda rauni, kuma an dauki gaba dayansu zuwa asibiti don yi musu magani.

Kofar Bab Huta dai hanya ce da ka iya kai mai bin ta Masallacin Al-Aqsa, wajen na 3 mai tsarki ga mabiya addinin Islama, inda mummunar tarzoma ta tashi a watan Mayun 2021 bayan da ’yan sandan isra’ila suka shiga harabarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.