Isa ga babban shafi
Koriya ta Arewa

Amurka ta dau tsauraran matakai kan gwajin makamin Koriya ta Arewa

Amurka ta kakaba wasu sabbin takunkumai kan kamfanoni da wasu ‘yan kasar  Rasha da Koriya ta Arewa bayan gwajin makami mai linzami mai cin dogon zango da kasar ta yi.

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jung Un.
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jung Un. REUTERS/KCNA
Talla

Ana zargin mutanen da kamfanonin da taimawa  wajen shigar da muhimman kayayyaki cikin shirin makami mai linzami na Koriya ta Arewa," a cewar wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar.

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un da ​​kansa ya sa ido a kan gwajin wani sabon nau'in makami mai linzami mai cin dogon zango da kasar ta yi jiya Alhamis, karon farko tun shekarar 2017, kuma da alama ya zarta gwaje-gwajen da ya yi a baya a cin dogon zago.

Makamin da aka wa lakabi da Hwasong-17,  wadda ke cin dogon zango an fara kaddamar da shi ne a shekarar 2020.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.