Isa ga babban shafi
China

'Yan sama jannatin China 3 sun dawo kasa bayan shafe wata 6 a sararin samaniya

Wasu 'yan sama jannatin kasar China uku sun koma doron kasa a wannan Asabar bayan shafe kwanaki 183 a sararin samaniya, lamarin da ya kawo karshen kumbo  mafi dadewa a kokarin China na zama jagaba a harkar sararin samaniya.

Kumban 'yan sama jannatin China da ya sauka a doron kasa bayan shafe watanni 6 a sararin samaniya,16/04/22.
Kumban 'yan sama jannatin China da ya sauka a doron kasa bayan shafe watanni 6 a sararin samaniya,16/04/22. AFP - -
Talla

Kumbon Shenzhou-13 shine na baya-bayan nan da kasar China ta aika duniyar Mars ya kuma aike da bincike zuwa duniyar wata a yunkurin ta na gogayya da Amurka a fannin.

Maza biyu da mace daya -- Zhai Zhigang da Ye Guangfu da kuma Wang Yaping -- sun dawo duniya ne da misalin karfe 10 na safe agogon Beijing, bayan da suka shafe watanni shida suna cikin jirgin Tianhe na tashar sararin samaniyar Tiangong na kasar China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.