Isa ga babban shafi
China-

Wadanda Korona ke kashewa a China suna karuwa

Birnin Shanghai a China ta sanar da mutuwar mutane 39 da cutar covid-19 ta kashe a yau Lahadi, adadi mafi yawa duk da da makonni da aka shafe ana kulle, a yayin da mahukuntan birnin Beijing suka yi gargadin cewa akwai yiwuwar ta’azzarar yaduwar cutar.

Jami'an kiwon lafiya a Shanghai na yin feshi don kashe kwayoyin cuta.
Jami'an kiwon lafiya a Shanghai na yin feshi don kashe kwayoyin cuta. AP - Nico de Rouge
Talla

Kasar, wadda ita ce  ta biyu a karfin tattalin arziki a duniya, tana ta kokarin shawo kan annoba mafi muni da ta addabe ta a cikin shekaru 2, inda ta yi ta kakaba dokokin kulle masu gauni, tare da gwaji ba kakkautawa.

Birnin Shanghai, wanda shine cibiyar kasuwancin China ya shiga yanayi na kulle a gaba daya watan da ya gabata, lamarin da ya sa mazauna garin zama a gida na tsawon lokaci fiye da yadda suka taba yi.

Birnin mai yawan al’umma miliyan 22, ya na ta kokarin samar da abinci mai inganci ga wadanda ke kulle a gidaje, a yayin da marasa lafiya keta korafin rashin  samun kulawa, sakamakon yadda aka aike da dubban malaman lafiya zuwa cibiyoyin gwaji da kula da masu Covid-19.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.