Korona ta kashe mutane 21 a Koriya ta Arewa a cikin sa'o'i 24
Koriya ta Arewa ta sanar da nutuwar mutane 21 a Asabar din nan, kana ta ce mutane rabin miliyan ne suka kwanta rashin lafiya a fadin kasar, kwanaki 2 bayan da ta tabbatar da sake bullar cutar Covid 19.
Wallafawa ranar:
Duk da kakaba dokokin kulle don dakile yaduwar cutar a tsakanin al’ummarta wadda da ba a wa rigakafi ba, Koriya ta Arewa tana samun dubban masu harbuwa da wannan cutar a duk rana.
A ranar Juma’a kadai, sama da mutane miliyan 174,440 ne suka kamu da cutar, kuma dubu 81, 430 sun murmure, a yayin da 21 suka mutu, kamar yadda kamfanin dillancin labarn Koriya ta Arewar ta ruwaito.
A ranar Alhamis Koriya ta Arewar ta tabbatarda cewa an samu bullar Omicron, nau’in cutar Covid-19 mai saurin yaduwa a babban birnin kasar Pyonyang, inda shugaba Kim Jong Un ya yi umurnin dokar kulle a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu