Isa ga babban shafi

Jirgin sama dauke da fasinjoji 22 ya bace a tsaunukan Nepal

Wani karamin jirgin saman a fasinja mallakin wani kamfani mai zaman kansa ya bace a tsakanin wasu dogayen tsaunuka a kasar Nepal a Lahadin nan.

Wani karamin jirgin saman fasinja a kusa da jerin manyan tsaunukan Himalaya daga bangaren kasar Nepal.
Wani karamin jirgin saman fasinja a kusa da jerin manyan tsaunukan Himalaya daga bangaren kasar Nepal. via REUTERS - MADHU THAPA
Talla

Bayanai sun ce jirgin saman dake dauke da fasinjoji 22 ya bace ne sakamakon rashin kyawun yanayi.

Gwamnatin kasar ta Nepal ta ce tuni aka aike da tawagar jami’an ceto zuwa wani yanki dake kusa da kogin Khola a gaban tsaunukan Himalaya, inda mazauna wurin suka sanar da ganin alamun tashin wuta.

jami’ai sun ce jirgin fasinjan ya tashi ne da safiyar yau Lahadi somin yin balaguron tsawon mintuna 20, amma sadarwa ta yanke tsakaninsa da masu kula da sufurin jiragen saman kasar mintun 5 kacal bayan tashinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.