Isa ga babban shafi

Kasashen Gulf sun yi tir da batanci ga musulunci da wata jami'ar India ta yi

Kasashen dake Yankin Tekun Fasha cikin su harda Saudi Arabia sun yi Allah wadai da kalaman mai Magana da yawun Jam’iyyar BJP dake mulkin India na batunci ga Annabi Muhammad wanda tsira da Amincin Allah suka tabbata a gare shi.

Kasashen dake Yankin Tekun Fasha cikin su harda Saudi Arabia sun yi Allah wadai da kalaman mai Magana da yawun Jam’iyyar BJP dake mulkin India na batunci ga Annabi Muhammad wanda tsira da Amincin Allah suka tabbata a gare shi
Kasashen dake Yankin Tekun Fasha cikin su harda Saudi Arabia sun yi Allah wadai da kalaman mai Magana da yawun Jam’iyyar BJP dake mulkin India na batunci ga Annabi Muhammad wanda tsira da Amincin Allah suka tabbata a gare shi AP - Rajesh Kumar Singh
Talla

Kalaman mai Magana da yawun jam’iyyar Firaminista Narendra Modi, Nupur Sharma ya haifar da arangama tsakanin al'umma wata jiha da kuma bukatar kama ta, yayin da kasashen Musulmi ke bayyana bacin ran su da matakin.

Saudiya ta yi Allah wadai

Saudi Arabia na daga cikin kasashen da suka soki kalaman Sharma lokacin da take mahawara ta kafar talabijin, inda ta bayyana kalaman a matsayin cin zarafi, yayin da ta bukaci mutunta addinan jama’a.

Ita ma kasar Qatar ta bayyana bacin ranta inda ta bukaci India ta nemi gafara akan kalaman, a dai dai lokacin da mataimakin shugaban kasar Indian Venkaiah Naidu ke ziyara a kasar domin bunkasa harkokin kasuwanci.

Kasar Qatar ma ta yi tir

Ma’aikatar harkokin wajen Qatar ta gayyaci Jakadan India Deepak Mittal domin gabatar da korafin ta a daidai lokacin da Naidu da wasu shugabannin Yan kasuwa ke ziyarar kasar.

Kasar Kuwait da kungiyar kasashe Musulmai sun bi sahu wajen bayyana bacin ransu da abinda suka kira cin zarafin Musulmi da addinin su.

An dakatar da Sharma

Daga bisani Jam’iyyar BJP ta sanar da dakatar da Sharma saboda abinda ta kira gabatar da manufofin da suka sabawa jam’iyyar, yayin da ta bayyana matsayin ta na mutunta addinai daban daban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.