Kasashen da ke cikin yarjejeninyar Abraham Accord za su yi taro a Bahrain
Jami'an diflomasiya daga Amurka da Israila da wasu kasashen Larabawa 4 za su taru yau a Bahrain domin tattauna ci gaban da aka samu a karkashin shirin zaman lafiyar Gabas ta Tsakiya da aka yiwa lakabi da ‘Abraham Accord’.
Wallafawa ranar:
Ana saran taron ya samu halartar jami’an ma’aikatar harkokin wajen kasashen Daular Larabawa da Bahrain da Morocco wadanda suka kulla yarjejeniyar hulda da Israila a shekarar 2020, sai kuma Masar wadda tun a shekarar 1979 take hulda da kasar.
Ita dai wannan yarjejeniyar da ake kira ’Abraham Accord’ ta harzuka Falasdinawa wadanda suka zargi kasashen Larabawan da suka sanya hannu a ciki da cin amana.
Kasar Amurka ta ce ta na bukatar gudanar da irin wannan taro kowacce shekara da zummar sasanta Yahudawa da Falasdinawa domin tabbatar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu