Isa ga babban shafi

Masu shaye-shaye fiye da 500 sun tsere daga cibiyar gyaran hali a Sri Lanka

Daruruwan fursunoni ne suka tsere daga wata cibiyar gyaran hali ta masu ta’ammali da miyagun kwayoyi a Sri Lanka bayan da suka lalata shingayen da aka sanya a wurin.

Wani sansanin killace masu shaye-shaye.
Wani sansanin killace masu shaye-shaye. Marvin RECINOS / AFP
Talla

Tashin hankali ya barke ne bayan da ‘yan sanda suka shiga cibiyar gyaran halin ta Kandakadu don gudanar da bincike kan mutuwar guda daga cikin su.

Sanarwar da rundunar ‘yan sandan kasar ta fitar ta ce, fiye da rabin wadanda ke tsaren sun tsere a lokacin tarzomar sai dai an kai wani samame a yankin domin cafke su.

Bayanai sun nuna cewa ya zuwa ranar 16 ga watan Yuni, akwai mutane 951 da ake tsare da su a cibiyar karkashin umarnin kotu, bayan da aka same su da laifukan da suka shafi ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Hukumomin lafiya sun ce an samu karancin magunguna masu mahimmanci, ciki har da wadanda ake amfani da su wajen kula da masu matsalar shaye-shaye, saboda tabarbarewar tattalin arzikin kasar Sri Lanka.

Al'ummar tsibirin dai na fama da matsanancin rashin kudi sakamakon rashin kudaden ketare da ake amfani da su wajen biyan kudin abinci da man fetur da magunguna da sauran kayayyakin masarufi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.