Isa ga babban shafi

Rikici ya barke tsakanin Taliban da wata kungiya dauke da makamai a Afghanistan

Rikicin da ya balle a tsakanin ‘yan Taliban da kuma magoya bayan wani tsohon kwamandan ta, dake yi mata tawaye a watan jiya ya tilastawa dubban mutane tserewa daga yankin arewacin kasar.

Wasu mayakan Taliban a wani yanki na kasar Afghanistan.
Wasu mayakan Taliban a wani yanki na kasar Afghanistan. AP - Mohammad Asif Khan
Talla

A zantawarta da manema labarai ba tare da ta bayyana sunanta na asali ba Zahra mai shekaru 35 a duniya tare da iyalanta sun kasance daga cikin dubban mutanen da suka tsere daga rikicin tsakanin mayakan Taliban da mayakan dake biyayya ga Mahdi Mujahid, tsohon shugaban leken asiri na Bamiyan.

Zahra da iyalan nata sun shafe tsawon kwanaki suna tsallaka tsaunuka dan tsira da rayukansu, ba tare da suna da tabbacin abinda zasu tarar ba.

Wani mai sharhi kan harkokin siyasa mazaunin Kasar Australia, Nematullah Bizhan, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa Kabilanci, da addini da kuma rikicin da ake yi kan batun samun albarkatun coal na yankin Balkhab sun kasance umul aba’isin tsanantar rikicin.

Kabilar Haara mabiya mazhabar shi’a na fuskantar muzgunawa tsawon shekaru, yayin da ake zargin ‘yan Taliban da kuntata wa wannan kabila tsakanin shekarar 1996 zuwa 2001.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.