Isa ga babban shafi

Duniya ta yi wa sojin Myanmar rubdugu kan kisan da suka yi

Majalisar Dinkin Duniya da Human Right Watch da Amurka da Faransa duk sun yi tur da kisan da gwamnatin sojin Myanmar ta yi wa wasu fursunoni hudu da suka masu rajin kare ‘yancin demokuradiya a kasar.

Jimmy da Phyo Zeya Thaw da aka kashe a Myanmar
Jimmy da Phyo Zeya Thaw da aka kashe a Myanmar via REUTERS - MRTV
Talla

Shugabar Hukumar Kare Hakkin Bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya, Michel Batchelet ta bayyana kisan da  aka yi wa fursunonin a matsayin zalunci da rashin wayewa, tana mai cewa, lallai ta kadu da al’amarin, duk da irin kiraye-kirayen da kasashen duniya suka yi wa sojojin amma suka yi biris har suka aiwatar da kisan.

Ita ma Faransa ta ce, wannan kisan wanda shi ne  karon farko da aka gani a Myanmar cikin shekaru 30, na nuni da gagarumin duhun-kai da kuma wani sabon babin da sojojin suka bude na aikata miyagun laifuka tun bayan da suka kwace mulki da karfin tsiya daga hannun  gwamnatin Aung San Suu Kyi.

Kazalika  wata sanarwa da ofishin jakadancin Amurka ya fitar a birnin Yangon,  ta yi tur da abin da sojojin suka yi na kisan shugabannin masu rajin kare ‘yancin demokuradiya  da wasu jami’an tsohuwar gwamnatin kasar.

Wadanda sojojin suka kashen sun hada da Phyo Zeya Thaw, tsohon dan majalisa kuma mamba a jam’iyyar tsohuwar shugaban gwamnatin kasar da aka yi wa juyin mulki, Aung San Suu Kyi.

Sai kuma fitaccen mai rajin kare demokuradiya a kasar, Kyaw Min Yu da aka fi sani da Jimmy da shi ma sojojin suka zartasa masa da hukuncin kisan.

Sai kuma wasu mutane biyu  da aka zarga da kisan wata mata da aka ce tana taimaka wa sojojin leken asiri a Myanmar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.