Isa ga babban shafi

Faransa ta bukaci EU ta ladabtar da jami'an Iran kan murkushe masu zanga-zanga

Faransa na neman kungiyar Tarayyar Turai ta dauki matakin ladabtarwa kan manyan jami’an gwamnatin Iran, sakamakon matakan da jami’an tsaron kasar ke dauka na murkushe zanga-zngar da dubban jama’a ke yi kan mutuwar matashiya Mahsa Amini a hannun ‘yan sandan gyaran tarbiya.

Mutane kusan dubu guda aka kame a zanga-zangar ta Iran.
Mutane kusan dubu guda aka kame a zanga-zangar ta Iran. © Fredrik Persson/via REUTERS
Talla

Ministan harkokin wajen Faransa Catherine Colonna ta ce takunkuman da ake neman a kakabawa manyan jami’an na Iran sun hada da kwace kadarorinsu da ke Turai, da kuma hana su tafiye-tafiye zuwa nahiyar.

Wasu majiyoyin diflomasiyya sun bayyana cewar tuni tattaunawa ta yi nisa tsakanin Faransa da Jamus da Denmark, da Spain, da Italiya da kuma Jamhuriyar Czech kan sabbin takunkumin da ake shirin kakabawa Iran.

Fusata kan mutuwar Mahsa Amini  wadda aka kama saboda rashin sanya Hijabi a Iran ya haifar da zanga-zanga mafi girma a kasar cikin kusan shekaru uku, yayinda matakin murkushe masu zanga-zangar ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 100 tare da kama wasu fiye da dubu guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.