Isa ga babban shafi

Taliban ta kafa lasifika 400 saboda kiran Sallah

Gwamnatin Taliban ta Afghanistan ta kafa amsa-kuwa ko kuma lasifika har guda 400 a sassan babban birnin kasar domin karfafa wa masu ibada guiwar halartar Masallatai da zaran an kira Sallah.

Wasu daga cikin jagororin Taliban
Wasu daga cikin jagororin Taliban AP - Ebrahim Noroozi
Talla

Ma’aikatar Yada Kyawawan Dabi’u ta Afghanistan ta ce, an mayar da daruruwan kufai na shaguna da gidaje zuwa Masallatai domin bai wa kowa da kowa damar yin Sallah a cikin unguwanni.

Ma’aikatar ta ce,  gwamnatin da ta gabata, ta cire wasu tarin amsa-kuwa da aka kafa a Kabul, abin da ya hana mutane sauraren kiran Sallah.

Tun bayan da ta karbe mulki a cikin watan Agustan bara, sannu a hankali Taliban ke ci gaba da kafa tsauraran dokoki da ta ce, sun yi daidai da shari’ar Musulunci.

Kazalika a karkashin jagorancin Taliban, an takaita wa mata walwala a bainal jama’a, yayin da dama daga cikinsu suka rasa guraben ayyukansu  ko kuma ake biyan su wasu kudaden alawus-alawus domin hana su fitowa daga gida.

Dole ne kuma matan su rufe fuskokinsu da nikabi ko hijabi gabanin fitowa daga gida , sannan Taliban ta haramta musu yin balaguro ba tare da muharrami ba.

Har wa yau, Taliban ta rufe makarantun ‘yan mata a sassan kasar tun bayan da mulki ya koma hannunta a watan Agustan bara.

A farkon watan nan ne, Jagoran Addinin Kasar, Hibatullah Akhundzada ya bai wa alkalai umarnin fara aiwatar da dokokin shari’ar Musulunci da suka hada da kisa da jifa da bulala da kuma gutsire hannayen barayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.