Isa ga babban shafi

China: Masu zanga zangar adawa da dokokin kulle sun yi arangama da 'yan sanda

Daruruwan masu zanga zanga sun yi arangama da ‘yan sanda a birnin shanghai, a yayin da ake ci gaba da  adawa da tsauraran matakan kariya daga cutar covid 19 da gwamnatin china ta dauka a kwana ta uku a jere, lamarin da ya bazu zuwa wasu birane da dama.

Masu zanga zangar adawa da dokokin kulle na Korona a China.
Masu zanga zangar adawa da dokokin kulle na Korona a China. REUTERS - THOMAS PETER
Talla

Zangar zangar ta baya bayan nan, irin wadda ba a taba yi ba tun da shugaba Xi Jinping ya dare karagar mulkin kasar shekaru 10 da suka wuce, ta fara ne bayan da mutane 10 suka mutu a wata  gobara a Urumqi, babban birin yankin yammacin kasar mai nisa na Xianjiang, wadda da dama suka dora alhakinta a kan tsauraran dokokin kulle na gwamnati don kariya daga cutar covid 19.

Wadannna mace mace sun kasance abin da  ya ingiza al’umma har suka nuna bacin ransu a kan tsauraran dokokin covid 19 da China ta dauka, gami da dokoki kulle masu tsauri, gwaje gwaje na gama gari,  da sa ido, wadanda suka ci gaba da kawo cikas ga harkokin yau da kullum na jama’a, shekaru 3 bayan bullar cutar corona a birnin Wuhan.

Daruruwan mutane sun taru a yammaci Lahadi a birnin, rike da kwalaye da ba a rubuta komai a kansu ba, a wani abu da ke nuni da yadda gwamnatin kasar ta  yi hani ga zanga zanga, a yayin da  dimbim ‘yan sandan da ke wajen suke ta mazurai.

Sauran biranen da aka gudanar da wannan zanga zangar a Lahadi sun hada da Lanzhou a arewa maso yammacin kasar, inda masu zanga zanga suka koka cewa sun dade a kulle, alhali kuwa babu wanda ya harbu da cutar Covid.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.