Isa ga babban shafi

Taliban ta haramtawa dalibai mata karatun jami'a a Afghansitan

Gwamnatin Taliban a kasar Afghanistan ta sanar da haramtawa dalibai mata karatun jami’a, a wani sabon mataki da ta dauka da ya shafi daukacin jami’oin gwamnati da masu zaman kansu. 

Wasu dalibai mata kenan da ke daukar karatu a kasar Afghanistan
Wasu dalibai mata kenan da ke daukar karatu a kasar Afghanistan AP - Ebrahim Noroozi
Talla

Wata sanarwar da ma’aikatar ilimin kasar ta gabatar ne ya bayyana daukar wannan sabon mataki na haramta karatun jami’a ga daliban mata na har illa masha Allahu. 

Mai magana da yawun ma’aikatar ilimin Ziaullah Hashimi ya gabatar da wannan sabuwar doka, wadda ake ganin zata dakushe aniyar dalibai mata na samun ilimi a cikin kasar. 

Haramcin karatun a jami’oin Afghansitan na zuwa ne kasa da watanni 3 bayan dubban dalibai mata sun zana jarabawar shiga jami’a a fadin kasar, yayin da wasu suka gabatar da takardun neman kwarewa a bangaren injiniya da kuma zama likita. 

Bayan karbe iko da Afghansitan a watan Agustan bara, kungiyar Taliban ta baiwa jami’oi umurnin aiwatar da sabbin dokoki da suka kunshi raba maza da mata a azuzuwa, yayin da aka baiwa malamai mata damar koyar da dalibai mata kawai. 

Rahotanni sun ce tuni gwamnatin kasar ta haramtawa dalibai mata da dama karatun sakandare, abinda ya taikaita yawan daliban dake samun damar zuwa jami'a, 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.