Isa ga babban shafi

Girgizar kasar mai karfin sama da maki 6 ta auku a Japan

Wata girgizar kasa mai kaarfin maki 6 da digo 1 ta auku a arewacin Japan a Talatar nan, sai dai babu wani kashedi a game da faruwar guguwar tsunami daga hukumar kula da yanayi ta kasar a yayin da ta yi wannan sanarwar.

Ana yawan samun girgizar kasa a Japan.
Ana yawan samun girgizar kasa a Japan. AFP/File
Talla

Hukumar hasashen yanayi ta Japan ta ce girgizar kasar ta auku ne da misalin karfe 6 da minti 18 agogon kasar, daidai da karfe 9 da minti 18 agogon GMT.

Manyan kafofin yada labaran Japan ba su bada labarin irin barnar da girgizar kasar ta yi ba, ko kuma wadanda suka ji rauni a sakamakon ta.

Girgizar kasa aba ce da ake yawaita yi a Japan, kasar da ke zaune a yanki mafi hatsari na tekun Pacific, wanda ake  wa lakabi da ‘Ring of Fire’, wato inda fayafayen tectonic biyu suka gamu, kuma mostinsu ke haddasa ambaliya ko girgizar kasa a kudu maso gabashin nahiyaar Asiya.

Kasar tana da tsauraran dokoki a kana bin da ya shafi gine-gine, domin a tabbatar da cewa gidaje a yankin sun samu juriya a duk lokacin girgizar kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.