Isa ga babban shafi

Turmutsutsu yayin karbar abincin sadaka ya kashe mutane 11 a Pakistan

Akalla mutane 11 suka mutu dukkaninsu mata da kananan yara yayin wani turmutsutsun karbar abincin sadakar azumi a kudancin birnin Karachi na Pakistan.

Musulmi a kasar Pakistan, bayan sayen kayan abincin da za su yi buda baki dasu a cikin azumin watan Ramadan.
Musulmi a kasar Pakistan, bayan sayen kayan abincin da za su yi buda baki dasu a cikin azumin watan Ramadan. AP - Shakil Adil
Talla

Jami’an da suka kai dauki wajen turmutsutsun sun ce mutane da dama sun jikkata a wajen rabon abincin na jiya juma’a ciki har da wadanda suka fada rijiya.

Jami’an ‘yan sandan da suka kai dauki wajen faruwar lamarin sun ce wani attajiri da ke da kamfani a yankin ne ya shirya bayar da abincin sadaka ga mabukata saboda azumin watan Ramadana.

A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan yankin attjirin bai sanar da hukumomi game da shirin nasa na rabon abinci azumi ba, dalilin da ya babu jami’ai na musamman da za su kula da cunkoson jama’a.

Sahidun gani da ido a wajen rabon abincin sun ce turmutsutsun jama’a sai da ya kai ga rushe katanga a kamfanin attajirin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.