Isa ga babban shafi

Amurka ta bukaci tasa keyar 'yan Korea ta Arewa da ke rayuwa a ketare zuwa gida

Kasashen Amurka da Japan da kuma Korea ta Kudu sun mikawa Majalisar Dinkin Duniya bukatar tisa keyar dukkanin al’ummar Korea ta Arewa mazauna ketare tare da mayar da su gida bisa ikirarin cewa ‘yan kasar na amfani da damar zamansu a ketare wajen tara kudin taimakawa Pyongyang don habaka haramtaccen shirinta na Nukiliya.

Majalisar zartaswar Korea ta Arewa.
Majalisar zartaswar Korea ta Arewa. via REUTERS - KCNA
Talla

Wakilcin kasashen 3 ya shaidawa Majalisar Dinkin Duniya, cewa ‘yan Korea ta Arewan da ke zaune a ketare na kuma aikata kutsen na’ura da kuma satar fasaha ta na’ura don tattara kudaden karawa kasar karfin Soji.

Korea ta Arewa wadda ke fuskantar manyan takunkuman karya tattalin arziki ta na samun kudaden shiga daga sojojin da ta ke horarwa tare da tura su kasashe don yin yakin kudi cikin kasashen kuwa har da Rasha da China baya wani yanki na Turai da gabas ta tsakiya da kuma Afrika.

Tun a shekarar 2017, mambobin majalisar bisa bukatar Amurka da kawayenta suka kada kuri’ar neman tisa keyar ‘yan Korea ta Arewan zuwa kasar su kafin watan Disamban 2019 amma kuma lamarin ya gaza tabbatuwa.

A baya-bayan nan Korea ta Arewa na ci gaba da habaka sashen makamin nukiliyarta inda ko a jawabin shugaba Kim Jun Un ya shaidawa dakarun Sojin kasar cewa su yi shirin yaki na gaske.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.