Gwamnatin Myanmar ta yi afuwa ga fursunoni fiye da 2,000 saboda bukin Buddha
Gwamnatin sojin Myanmar ta sanar da yin afuwa ga fursunoni fiye da dubu 2 da aka daure karkashin wata doka da aka yi amfani da ita wajen murkushe 'yan adawa tun bayan da ta kwace mulki fiye da shekaru biyu da suka gabata.
Wallafawa ranar:
Sojoji sun kama dubban masu zanga-zanga da masu fafutuka tun cikin watan Fabrairun shekarar 2021 wanda ya jefa kasar cikin rudani.
Sanarwar da gwamnati ta fitar ta nuna cewa ahuwar ta shafi fursunoni 2,153 da aka yanke hukunci a karkashin dokar hukunta manyan laifuka ta 505 (a) sabado bikin tunawa da ranar haihuwar Buddha ta Kasone Full Moon Day", a turance.
Dokar ta tanadi zaman yarin akalla shekaru uku, amatsayin mafi girman hukunci.
Bisa al’adama kasar Myanmar na yin ahuwa ga dubban fursunoni a irin yanayin bukukuwa da suka shafi kasa ko na addinin Buddah.
Ziyarar jami'in China
Sanarwar na ranar Laraba ta zo ne a daidai lokacin da ministan harkokin wajen kasar China Qin Gang ke ziyara domin tattaunawa da janar-janar masu mulkin kasar da ke zama saniyar ware ga manyan kasashen duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu