Isa ga babban shafi

Mutane 54 sun mutu a rikicin kabilanci a India

Adadin mutanen da suka mutu a rikicin kabilanci a yankin arewa maso gabashin India ya kai 54 a wannan Asabar, inda sabon fada ya barke a cikin daren da ya gabata duk da cewa an girke dubban jami'an tsaro domin maido da doka da oda.

Wani bangare da aka yi rikicin kabilanci a jihar Manipur ta India
Wani bangare da aka yi rikicin kabilanci a jihar Manipur ta India REUTERS - STRINGER
Talla

Hukumomin kasar sun girke dubban sojoji a jihar Manipur bayan zanga-zangar da wata kabila ta gudanar ta rikide zuwa tarzoma a ranar Laraba.

An kuma bai wa sojojin izinin harbi kai tsaye da zaran lamari ya ci tura domin lafar da rikicin, sannan tuni aka katse hanyoyin sadarwar intanet.

Sai dai wannan tarzoma ta kazance a ranar Juma'a cikin dare, sa'o'i kalilan da gargadin da babban jami'in 'yan sandan jihar ya yi na cewa, masu zanga-zangar sun sace makamai da harsashai daga ofisoshin 'yan sanda.

Kafafen yada labarai na cikin gida sun rawaito cewa, akalla akwai jumullar gawarwakin mutane 54 da aka ajiye su a asibitoci da ke jihar.

Wannan jiha ta Manipur ta yi kaurin suna a fannin rikicin kabilanci, inda aka kiyasta cewa, akalla mutane dubu 50 ne suka mutu tun daga tsakan-kanin 1950 sakamakon irin wannan rikicin mai nasaba da kabilanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.