Vietnam ta fuskanci yanayin zafi mafi muni a tarihinta
Vietnam ta sanar da yanayin zafi da ba a taba fuskanta ba a kasar a daren Asabar, wanda ya kai digiri 44 da digo 1 a ma’aunin Celsius, ko kuma 111 da digo 38 a ma’aunin fahrenheit, lamarin da ya zarce wanda aka fuskanta a shekarar 2019.
Wallafawa ranar:
Tun daga watan Afrika kudancin nahiyar Asiya ke fama da yanayi na tsananin zafi, inda kasashen da ke makwaftaka da nahiyar suka samu nasu rabon na zafi.
Yanayi a arewacin Veitnam ya banbanta da na kudancin kasar, amma a halin da ake cikin ilahirin kasar na fuskantar watanni mafi zafi a tarihi.
Da ranar Asabar din nan ne aka auna wannan yanayi na tsananin zafi mafi yawa a tarihin kasar, ta tashar Hoi Xuan a lardin Thanh Hoa arewa maso tsakiya, kamar yadda cibiyar hasashen yanayi na kasar ta bayyana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu