Isa ga babban shafi

Mutane 275 ne suka mutu a hadarin jirgin kasan India

Gwamnatin India ta ce mutane 275 ne suka rasa rayukansu sakamakon hadarin jirgin kasan da ya faru a kasar, hadarin da rabon da a ga mai muninsa tun shekaru 20 da suka gabata.

Wurin da aka samu hatsarin jirgin kasa a India
Wurin da aka samu hatsarin jirgin kasa a India AP - Arabinda Mahapatra
Talla

Kawo yanzu mutane 275 ne suka mutu, yayin da wasu 1,200 suka gamu da munanan raunuka a wannan hadari mafi muni da kasar ta gani.

Hadarin ya faru ne a yankin Balasore da ke gabashin kasar, bayan da wasu jirage biyu suka yi taho mu gama, sannan daya daga cikinsu ya tsallaka ya kuma samu wani jirgin kasan da ke tafiya a dayan hannun, lamarin da ya haifar da wannan mummunan raunin.

Duk da wannan adadi da gwamnatin ta bayar, da dama daga cikin al’ummar kasar na kokawa game da rashin ganin ‘yan uwansu, dalilin da ya sa gwamnati ta tattara sassan jikin mutanen da aka kasa gane su don yi musu gwajin kwayoyin hallita da nufin tabbatar da ‘yan uwansu.

Ministan Kula da Sufurin Jirgin kasa na India Ashwini Vaishnaw, ya ce a yanzu za a ci gaba da sufurin jiragen kasa, bayan sa’o’i 51 da faruwar wancan hadari, duk da dai babu cikakken bayani a game da gyaran titin jirgin da ya lalace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.