Isa ga babban shafi

Mutane 31 sun mutu sakamakon fashewar gas a China

Akalla mutane 31 ne suka mutu, kana wasu 7   suka jikkata sakamakon fashewar tukunyar iskar gas da ake amfani da ita wajen yin girki a wani gidan abinci da ke arewa maso yammacin China a daren Laraba.

Mutane da suka taru bayan fashewar gas din.
Mutane da suka taru bayan fashewar gas din. Reuters
Talla

Fashewar ta auku ne da misalin karfe 8 agogon China a wata unguwa mai yawan cinkoson jama’a a garin Yinchuan, babban birnin Ningxia Hui, inda akasarin al’ummar wurin Musulmi ne, kamar yadda  kamfanin dillancin labaran yankin ya ruwaito.

Lamarin ya auku ne a daidai ‘lokacin da al’umma suka taru don gudanar da bikin Dragon Boat Festival, na tunawa da  mutuwar wani fitaccen marubuci kuma ministan kasar,  Qu Yuan, wanda ya rayu a tsakanin shekarar 340–278  kafin zuwan Annabi Isa.

Kamfanin dillancin labaran Xinhua ya ruwaito cewa ana tsaka da gasa nama ne wannan al’amari ya auku, yana mai nanata adadin mutanen da suka rasu da wadanda suka samu munanan raunuka.

Hotunan bidiyo daga kafar talabijin kasar ta CCTV sun nuno yadda jami’an aikin kashe gobara suke da kokarin kashe wutar da ta tashi, a yayin da hayaki ke fitowa daga wata kafa ta ginin gidan abincin.

Shugaban China, Xi Jinping ya bukaci a gaggauta daukar matakin bai wa wadanda suka jikkata magani, tare da karfafa matakan sanya ido a kan manyan masana’antu da zummar kauce wa aukuwar irin wannan al’amari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.