Isa ga babban shafi

hadarin jirgin kasa a Pakistan ya yi sanadiyar mutuwar mutane 28

Akalla mutane 28 ne suka mutu a wani hadarin jirgin kasa da aka samu a kudancin Pakistan, bayan da jirgin kasa dauke da fasinjoji ya kauce daga kan haryarsa, a lokacin da yake kan tafiya. 

Oito vagões do trem Hazara Express saíram dos trilhos perto da cidade de Nawabshah, no sul do Paquistão, neste domingo, 6 de agosto de 2023.
Oito vagões do trem Hazara Express saíram dos trilhos perto da cidade de Nawabshah, no sul do Paquistão, neste domingo, 6 de agosto de 2023. AP - Pervez Masih
Talla

Ministan sufurin jiragen kasa na Pakistan Khawaja Saad Rafique ya baiyana cewa,  bayan wadanda suka mutu a hadarin an gaggauta kai wadanda suka jikkata asibiti domin basu kulawar da ta kamata. 

Fuskantar matsalolin hadarurruka dai a kasar  Pakistan, wani abu ne da aka saba gani, musamman na jiragen kasa na kasar dake fama da matsaloli na tsari, wadda ke da akalla tsawon kilomita dubu 7,500, da kuma ke daukar nauyin kai komon fasinjoji miliyan 80 a kowacce shekara. 

Rafique ya ci gaba da cewa, jirgin da ya kauce kan hanya, ya fuskanci matsalar ce, ba tare da hukumar sufurin jiragen ta samu wani rahoto kan wata matsala dangane da hayar da hadarin ya faru ba. 

Ministan ya kuma jaddada cewa,  tuni aka sanya dokar ta baci a asibitin da aka kai wadanda suka jikkatan domin ganin sun samu cikakkiyar kula ba tare da sun wahala ba. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.