Isa ga babban shafi

'Yan sandan Pakistan sun kama mutane fIye da 100 saboda tarzomar addini

Mahukuntan Pakistan sun cafke mutane sama da 100 sakamakon zargin su da hannu a tayar da tarzomar da suka alakanta ta da addini.

Wasu jami'an 'yan sandan Pakistan da ke sintiri
Wasu jami'an 'yan sandan Pakistan da ke sintiri Reuters/Akhtar Soomro
Talla

Tun farko mutanen mabiya addinin Musulunci dauke da makamai ne suka afka wa wasu majami’u guda hudu inda suka banka musu wuta sakamakon zargin mabiya addinin kirista da cin zarafin addinin Islama ta hanyar yaga Al-qur’ani.

Baya ga kona guraren ibadar kirista din, mutanen sun kuma lalata gidan guda daga cikin wadanda ake zargi da cin zarafin Al’qu’anin.

Bayanai sun ce har wayewar garin yau majami’ar The Historic Salvation Army Church da mutanen suka kona tana da ci da wuta.

Tun faruwar wannan lamari a jiya Laraba ne gwamnatin kasar ta sanar da haramta taron addini na tsawon kwanaki 7 a yankin Faisalabad ciki har da kauyen Jaranwala inda lamarin ya faru.

Har yanzu dai ba’a kama mutane biyun da ake zargi da cin zarafin Al’Kur’anin ba, duk da dai mahukunta sun ayyana abin da suka yi a matsayin sabo, dalili kenan da ya sa mutanen suka yanke hukuncin daukar doka a hannun su.

Har yanzu dai kasar Pakistan ba ta taba yanke wa wani mutum hukunci don an kama shi da laifin sabo ba, duk da cewa hakan laifi ne bisa dokokin kasar, wannan ce ta sa a mafi yawan lokaci jama’a ke daukar doka a hannunsu.

Ko a shekarar 2009 sai da wasu mutane a yankin Punjab na kasar suka kashe wani mutum dan asalin Sri Lanka ta hanyar banka masa wuta, bayan da aka zarge shi da batanci ga addinin islama, lamarin da ya juye zuwa tarzomar da ta yi sanadin kona gidaje fiye da 60.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.