Isa ga babban shafi

Indonesia ta kama wasu 'yan China 88 da laifin zamba a Soyayya

Mahukuntan Indonesia sun sanar da kame wasu ‘yan China 88 wadanda aka samu da laifin zamba a soyayya ta shafin intanet, inda bayanan suka nuna yadda suka yaudari tarin mutane tare da karbar makuden kudade.

Zamba a soyayya don samun kudade na ci gaba da tsananta tsakanin kasashen Asiya.
Zamba a soyayya don samun kudade na ci gaba da tsananta tsakanin kasashen Asiya. EUTERS/Kim Kyung-Hoon
Talla

Rundunar ‘yan sandan Indonesia ta ce an kame mutanen su 88 da suka kunshi mata 5 da maza 83 a birnin Batam na lardin tsibirin Riau a jiya Laraba kuma kai tsaye za a tisa keyarsu zuwa kasar su China.

‘Yan sandan na Indonesia sun ce dukkanin ‘yan Chinar su 88 na amfani da kafar Intanet wajen yaudarar mutane da sunan Soyayya ta yadda su ke tatsar makuden kudi daga garesu.

Sanarwar rundunar ‘yan sandan ta ce galibi wannan tawaga ta mayaudara ta fi mayar da hankali kan baki da suka shigo kasar daga China ko kuma manyan kusoshin gwamnatin Chinar da ke can Beijing ta yadda su ke musu dadin baki har su kai ga fadawa komar soyayyarsu.

A cewar sanarwar mayaudaran na amfani da salon nuna tamkar su na matukar son mutum da gaske kuma da zarar an fada komar su, sai su yi amfani da damar wajen yin hirarrakin batsa ko na rashin da’a ko kuma nadar bidiyo na rashin da’a daga bisani kuma su yi amfani da shi wajen barazanar sakinsa ga shafukan sada zumunta matukar ba a basu kudi ba.

Sanarwar 'yan sandan na Indonesia ta ce kaso mai yawa na jami'an gwamnati ko kuma kusoshin manyan ma'aikatu ko kamfanoni na Chinar sun fada komar irin wannan yaudara.

Galibin masu zamba ta shafukan Intanet sun fantsama kasar ta Indonesia da sauran kasashen kudu maso gabashin Asiya bayan da China ta kaddamar da wani sumamen kame masu damfara ta Intanet.

Ko a shekarar 2019 sai da mahukuntan Indonesia suka kame ‘yan China 85 da wasu ‘yan kasar 6 da ke aikata damfara da sunan soyayya ta shafin intanet wanda ya kai su ga karbar miliyoyin daloli daga hannun wadanda suka fada komarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.