Isa ga babban shafi

Kotu ta yankewa dan gwagwarmayar Thailand hukuncin daurin shekaru 4 a gidan yari

Kotu a kasar Thailand ta yankewa guda daga cikin ‘yan gwagwarmayar tabbatar da kasar kan tsarin dimokradiyya hukuncin daurin shekaru 4 a gidan yari sakamakon samun sa da laifin muzanta sarkin kasar.

Hoton Anon Munpa kenan da yayi subul da baka wajen zagin sarki
Hoton Anon Munpa kenan da yayi subul da baka wajen zagin sarki Lillian SUWANRUMPHA/AFP
Talla

Kasar Thailand na cikin kasashen da suka tanadi dokoki masu tsauri kan masu cin zarafin masarauta da iyalan ta, abinda zai iya kaiwa har ga yanke wa mutum hukuncin kisa matukar aibatawar ta yi muni.

Bayanai sun ce kotun ta sami Anon Munpa mai shekaru 39, wanda tsohon lauya ne, kuma gwagwarmayar kwatar hakkin dan adam da laifin zagin sarki kai tsaye a wajen wata zanga-zanga da ya jagoranta a bara.

A yayin zanga-zangar da Anon ya jagoranta yayi kalaman da ke bukatar a sake tsari ko kuma rage tasirin da masarauta ke da shi, tare da yiwa wasu dokokin kasar da suka fifita masarauta kwaskwarima, inda a cikin kalaman ne kuma ya zagin sarki, laifin da zai iya kaiwa har ga yanke masa hukuncin shekaru 15 a gidan yari.

Bayan wadannan kalamai ne kuma Anod ya daga yatsun sa guda uku, alamar da aka haramta amfani da ita a kasar wadda ta samo asali daga cikin wani Film mai taken hunger games da aka dauke shi matsayin raini ga masarauta.

Da yake yiwa magoya bayan sa jawabi bayan yanke masa hukuncin Anon ya ce gwamnati zata iya yanke masa hukunci, amma baya nadamar gwagwarmayar da yake yi wadda yace ba zai tsaya ba, sai ya tabbatar da kafuwar ingantacciyar dimokradiyya.

Bayan wannan hukunci na shekaru hudu a gidan yari, kotun ta kuma ci shi tarar kudin kasar har baht dubu 20.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.